Saturday, 30 January 2016

Yanda Zaka Canza addreshin Ip dinka A Komfiyuta Na Windows

Yanda Zaka Canza addreshin Ip dinka A Komfiyuta Na Windows
Barkan Mu Da Warhaka. Yau Nazo Manah Da Yanda Zaka Canza IP
address A komfiyuta . Ko wanna Dan Adam, Yana Dana Sa Dalilai
Akan Meya Sa Zai canza IP address wasu Sabida Tsaro Wasu kuma
Dalilin Su Ka Dai Suka Sani. Amma Nidai Nayi Ne Domin Al'Umma
Su Amfana...

A Takaice Meye IP Address
Wato dai Ip address Wani Hanya ce Wanda Take Nuna Na'urar da
take yin Amfani da Ita.. kuma Kowacce Na'urar

[misali: Komfiyuta
da Waya Sailula] Suna Da Nasu IP Address Na dabam .. Ana iya
gano inda ake amfani da na'urar ta wannan IP din..
Yanda ake Canza IP Address
1. Danna Akan Start Sai kuma Ka Danna Akan Control Panel
2. Zabi Network da kuma Internet.
3. Danna akan Network and Sharing Centre.
4. Zabi Canza adapter settings a sashi na Hagu.
5. Yanzu Kayi Right Click akan Network din ka kuke haduwa na
Sadarwa Yanar Gizo [ Connecting] a lokacin.
6. Zabi Properties
7. Yanzu Sai ka Danna Sau biyu [Double Click] akan Internet
Protocol Version 6(TCP/IPv6)
8. Yanzu Sai Ka Zabi Yin Amfani Da Wa'innan IPv6 address:
9. Yanzu Sai Ka Sanya Ko wanna Irin Ip address Kake So a gurin
10. Ka danna Sau biyu akan Madanni Wanda Yake Nuna Mai Amfani
Ne [Valid Bottom] Sai Ka danna OK
Karin Bayani
Yanzu Ko Ina Kake Amfani Network Zaka dunga amfani da wanna IP
din daka Canza.. sai kuma Idan Kana Son Ka Maida Shi Na Asali
Kawai Sai Ka Yanda Nayi Bayanin Nan Sai Ka danna Akan Obtain an
Ipv6 address automatically sai ka Danna OK..
Shikenan Ka Canza Ip Address Dinka Na Windows Komfiyuta....
Idan akwai abin Baka Gane Ba koko Kana Son Ai maka Bayani Akan
Yanda Zaka Canza Irin Na Komfiyuta Dinka Idan Ba Windows Bace
Sai Ka Sanar Damu Akan Lokaci....
Ahuta Lapia........

Blogger
Disqus
Pilih Sistem Komentar Yang Anda Sukai

No comments

Disclaimer: Opinions expressed in comments are those of the comment 💬📝writers alone and does not reflect or represent the views of CLICKNAIJ Blog🚯