Sunday, 10 September 2017

FYADE: Mata ‘Yan Jarida sun gudanar da zanga-zanga a jihar Filato

Tags
Kungiyar ‘Yan Jarida Mata, reshen Jihar Filato sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwar su dangane da yawaitar yi wa mata da kananan yara fyade a kasar nan.
Sun gudanar da wannan jerin-gwano ne a kasuwannin garin Jos, babban birnin jihar Filato.
A jawabin ta, Shugabar Kungiyar ta Jiha, Madam Jennifer Yerima, ta nuna damuwa da matukar takaici ganin yadda ake samun yawaitar yi wa kananan yara fyade, musammam kanana da jirajirai. Ta ce wannan abin takaici ne, abin kunya ne kuma abu ne da al’umma ya kamata gaba daya a tashi tsaye a shawo kan sa. Ta kuma kara da cewa duk alamomin gushewar imani ne daga zukatan mazaje.
Ita kuwa Shugabar Gidauniyar Diamond Support Foundation, Adefunke Agina, wadda da hadin guiwar gidauniyar ta su aka yi gangamin, ta yi kira da a rika zartas da hukuncin kisa kai tsaye ga duk namijin da aka kama ya yi wa mace, karamar yarinya ko yaro fyade.
Ta ce “duk yaro ko yarinyar da aka yi wa fyade, to an fa riga an kassara ta, an tauye mata rayuwar ta kuma har ta mutu abin zai rika damunta a rayuwar su.’
Daga nan sai ta yi kira ga iyayen kananan yaran da aka yi wa fyade su rika fitowa su na fallasawa domin hukuma ta rika daukar mataki.
Ita kuwa Tsohuwar Sakatariyar Kungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Kasa, kira ta yi ga jami’an tsaro da su kara sa ido sosai wajen bai wa rahotanni da koke-koken da suka danganci fyaden mata da kananan yara muhimmanci.


Blogger
Disqus
Pilih Sistem Komentar Yang Anda Sukai

No comments

Disclaimer: Opinions expressed in comments are those of the comment 💬📝writers alone and does not reflect or represent the views of CLICKNAIJ Blog🚯