Friday, 29 June 2018

Gobarar motar dakon mai ta kashe mutane a Legas

Tags
Wata tankin dakon mai ta kama da wuta a Legas da ke Najeriya, inda jami'ai suka ce gobarar ta kashe akalla mutum tara.
Sama da motoci 50 ne wadanda suka hada da bas-bas, suka kama da wuta a lokacin da motar makare da mai ta kufce, sannan man da take dauke da shi ya malale a kan hanya.
An ce motar ta fadi ne sanadiyyar katsewar burki.

Gobarar motocin dakon mai abu ne da aka saba gani a Najeriya, wadda ita ce kasar da ta fi kowacce fitar da mai daga Afirka zuwa kasuwannin duniya.
Ana safarar irin wannan mai ne ta hanyoyin mota a kasar, wadanda ba su cika samun kulawa ba.
Gobarar ta ranar Alhamis, ta faru ne da misalin karfe biyar da rabi na yamma, a kan babbar hanyar da ta tashi daga Ibadan zuwa cikin birnin na Legas.Blogger
Disqus
Pilih Sistem Komentar Yang Anda Sukai

No comments

Disclaimer: Opinions expressed in comments are those of the comment 💬📝writers alone and does not reflect or represent the views of CLICKNAIJ Blog🚯